6 Oktoba 2025 - 22:54
Source: ABNA24
Shahadar "Hasan Adwi" Da Matarsa ​​A Harin Da Isra'ila Ta Kai A Kudancin Lebanon + Bidiyo.

Gwamnatin Isra'ila ta kai hari kan motar da ke dauke da "Hassan Adwi" daya daga cikin wadanda suka jikkata a harin wayoyin Pager da matarsa ​​"Zeinab Raslan" a garin Zabdeen da jirage marasa matuka.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbayt {As} –ABNA- ya bayar da rahoton cewa: Cibiyar kula da agajin gaggawa ta kasar Lebanon ta tabbatar da cewa mutane biyu ne suka yi shahada yayin da wani dan kasar Lebanon guda ya jikkata a harin.

An kai harin ne a lokaci guda tare da kai harin bam a gabashin Lebanon da kuma ikirarin Tel Aviv na cewa ta kai harin ne ga daya daga cikin kwamandojin sashin Ridwan na Hizbullah.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha